Nasir Abbas Babi
Radio Producer, Teacher, and Filmmaker in Sokoto, Nigeria
Nasir Abbas Babi
Radio Producer, Teacher, and Filmmaker in Sokoto, Nigeria
Nasir Abbas Babi, haifaffen garin Sakkwato ne a Shiyar Assada, An haife shi a 03/03/1990. kafin Karatunsa na Sakandare a makarantar Hardar Alqur'ani da sauran Karance-karance ta Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya halarci makarantar Magajingari Model Primary School da ke shiyar Assada.
Nasir Abbas Babi marubuci ne kuma manazarci akan al'amuran da ke kai komo, nayau da kullum. Ya yi rubuce-rubuce da dama a Jaridun Kasar Najeriya irin su Aminiya, Mujallar Siyasa, Rariya jarida da Leadership Hausa. Ya kuma kammala karatunsa na Diploma akan Na'ura mai kwakwalwa (Computer) kafin zuwansa Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, inda ya kammala digirinsa akan nzarin addinin Musulunci. Kafin kammalawar kuma, sai da ya rike mukamin shugaban kungiyar daliban nazarin Addinin Musulunci ta kasa (UDUS CHAPTER)
Nasiru Abbas Babi ya fara aiki da makarantar Adiya Islamiyya a shekarar 2008, a matsayin malamin makaranta mai koyar da Al-Qur'ani. Daga nan ya zama shugaban aji, zuwa shugaba (H.O.D) na sashen general studies da kuma school activities. Bayan nan kuma, an zabe shi inda ya rike ofishin Dean, daga baya kuma aka zabe shi domin rike ofishin da ke kula da kudi na makarantar (Director Finance and supply.
A shekarar 2017, Nasir ya fara aiki da Caliphate Radio da ke Sakkwato, inda ya rike mukamin Head of producers, daga baya kuma ya dawo Garkuwa Fm Sokoto, inda yanzu haka ya ke rike da mukamin manajan sashen shirye-shirye.